Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Wasanni

Manyan kungiyoyin wasanni su rinka tallafawa kanana-Sarkin Kano

Published

on

Mai martaba sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya bukaci kungiyoyin wasannin na kasar nan da su rika tallafawa kananan kungiyoyi domin farfado da su.

Sarkin ya bayyana hakan ne a ranar 17 ga watan satumbar shekarar 2021 lokacin da kungiyar kwallon Polo ta Kano ta kai masa ziyara fadar sa.

Aminu Ado Bayero ya ce idan manyan kungiyoyi na taimakawa kananan za’a samu ci gaban da ya kamata.

A nasa jawabin Shugaban kungiyar kwallon Polo na jihar Kano, Alhaji Bashir Sunusu Dantata ya ce sunzo fadar ne domin sarki yasa musu albarka.

Ziyarar ta samu wakilcin ‘yan wasan Polo daban daban dake ciki da wajen Kano.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!