Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

ilimi

Marasa kishin kasa da son lalata harkar ilimi ne suka fitar da wata kalandar bogi – Ganduje

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta bukaci jama’ar jihar da su yi watsi da wata sabuwar kalandar jadawalin karatun firamare da sakandire ta bogi da ke yawo tsakanin jama’a.

Kwamishinan ilimi Malam Muhammad Sanusi Sa’idu Kiru ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar.

Ya ce, wasu mutane ne da ke son karkatar da hankalin jama’a ne suka samar da kalandar, a don haka ma’aikatar ilimi bata da masaniya kan yadda kalandar ta samo asali.

Muhammad Sanusi Kiru, ya kara da cewa akwai bukatar iyaye su kula wajen tantance kalandar ilimi ta gaskiya da ta bogi, domin kuwa akwai marasa kishin kasa da ke son lalata harkar ilimi a jihar Kano.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!