Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

APC – Nan ba da jimawa ba Buhari zai yi maganin ‘yan ta’adda da masu daukar nauyinsu

Published

on

Jam’iyyar APC ta ce nan ba da jimawa ba shugaban kasa Muhammadu Buhari zai yi maganin ‘yan ta’adda da ke zubar da jinin al’umma babu gaira babu dalili a kasar nan har ma da masu daukar nauyinsu.

 

A cewar jam’iyyar halin rashin tsaro da ke addabar kasar nan a wannan lokaci lamari ne da jam’iyyar ba za ta mai da shi batu na siyasa ba, kamar yadda ‘yan adawa ke yi.

 

Hakan na cikin wata sanarwa ce mai dauke da sa hannun sakataren yada labaran jam’iyyar Sanata John Akpanudoedehe.

 

Sanarwar ta ce rashin tsaro da kasar nan ke fuskanta a wannan lokaci musamman ta’addancin Boko Haram, masu satar mutane suna garkuwa da su da sauran tsageru da ke neman daidaita kasar nan ba za su samu nasara ba

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!