Connect with us

Labaran Wasanni

Mariri Market Cup: Layin Sunusi Dan Mande ya tsallaka zuwa wasan na kusa dana Karshe

Published

on

A Ci gaba da gasar cin kofin Mariri Cola Nut Market, da ake kira da Chairman Cup, wasan da aka buga a ranar Juma’a 1 ga watan Oktobar 2021 tsakanin kungiyar kwallon kafar Layin Sunusi Dan Mande da Layin ‘Yan Bage.

Layin ‘Yan Bage ya yi rashin nasara a hannun Layin Sunusi Dan Mande da ci 1-0.

Dan wasan Layin Sunusi Dan Mande Malam Dogo ne ya zura kwallon data basu nasara a mintuna 20 da fara wasan.

Nasarar da Layin Sunusi Dan Mande ya samu ya bashi damar zuwa wasan na kusa dana Karshe a gasar.

Mai horar da ‘yan wasan Layin Sunusi Dan Mande Halilu 02 ya ce jajircewar da ‘yan wasan sa suka nuna a wasan ne ya basu damar tsallakawa zuwa wasan na kusa dana Karshe.

Yayin da shi kuma mai horar da ‘yan wasan Layin ‘yan Bage Auwalu Ado ya ce dama ita kwallo farace da baka kuma sun karbi rashin nasarar da sukayi.

A ranar Lahadi 03 ga watan Oktobar 2021 za’a ci gaba da gasar cin kofin na Mariri Cola Nut Market da ake kira da Chairman Cup tsakanin Layin Bashir Roja da FC Kwata duk a kasuwar ta Mariri.

Wasan da za’a take da misalin karfe 4 da rabi na ranar a filin Sakandaren Mariri.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!