Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Masu bayar da abinci a cikin jiragen sama sun dawo bakin aiki – Hadi Sirika

Published

on

Ministan Sufurin Jiragen Saman kasar nan sanata Hadi Sirika, ya ce, a yanzu ayyukan masu bayar da abinci a cikin jirage zai ci gaba, biyo bayan dakatar da su da aka yi sakamakon annobar corona.

Sirika ya bayayana hakan ne a taron kwamitin kar-ta-kwana mai yaki da cutar corona na shugaban kasa a jiya Litinin 22 ga watan Maris din 2021.

A cewar Ministan, an dauki matakin ne bisa la’akari da kamfanonin da suka hada hannu wajen samar da kayan shakatawa a cikin jirgin wanda dakatarwar ta yi tasiri matuka.

Ya ce duk da haka, akwai hanyoyin da za a bi don sake dawo da ayyukan cikin jiragen sama na Najeriya wanda zai yi daidai da tsarin kasa da kasa.

Sirika ya sake jaddada shirin ci gaba da zirga-zirgar jiragen sama na kasa da kasa a Filin jirgin sama na Malam Aminu Kano, da na Akanu Ibiam da ke Enugu da na Fatakwal.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!