Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Coronavirus

Masu cutar Corona 231 suka rage a Kano

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta tabbatar da cewa, a ranar Larabar an yiwa mutane 427 gwajin cutar Corona, kuma sakamako ya nuna cewar 4 daga ciki suna dauke da cutar.

Ma’aikatar lafiya ta Kano ta sanar a shafinta na Twitter cewa, mutum 1,318 ne aka tabbatar sun kamu da cutar Corona a jihar, cikin mutum 18,574 da aka yiwa gwajin cutar a Kano.

Mutum 1,035 ne suka warke sarai daga cutar a Kano.

Sai mutum 52 da suka samu shahada sanadiyyar ta.

Ma’aikatar lafiyan ta Kano ta ce zuwa yanzu masu dauke da cutar 231 ne ke ci gaba da samun kulawa daga jami’an lafiya.

Wannan na zuwa ne, kwana guda bayan da gwamnatin jihar ta sanar da cewa mako biyu kenan ba tare da an samu wanda ya rasa ransa sanadiyyar cutar ba.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!