Labarai
Masu garkuwa da mutane sun sace dan jaridar Borno

Wasu ‘’Yan garkuwa sun sace wani dan jarida da ke aiki da gwamnatin jihar Borno, Abdulkarim Haruna.
An dai sace wannan dan jarida ne a a jiya litinin da misalin karfe uku zuwa hudu na yammancin jiya, a yayin da yake tafiya daga babban birnin tarayya Abuja zuwa jihar Bauchi.
Abdulkarim Haruna dai ya hau motar Bauchi daga tashar Nyanya a Abuja, tuni dai direban motar ya kai jakarsa da wayarsa ofishin yan sanda dake Jagindi a jihar Kaduna.
Direbar motar ya ce masu garkuwar na sanye da kayan sarki inda suka dauke dan jaridar