Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Garkuwa da Mutane: An ceto mutane 19 a jihar Katsina

Published

on

Gwamnatin jihar Katsina ta ce jami’an tsaro sun yi nasarar ceto mutane 19 cikin 20 da masu garkuwa da mutane suka  yi garkuwa da su.

Tun da fari dai masu garkuwa da mutanen sun tare motar bas dun da mutanen ke ciki a kan hanyar su ta shiga Minna daga jihar Katsina, inda kuma suka yi garkuwa da su.

Rahotanni sun bayyana cewa masu garkuwa da mutanen sun  yi garkuwa da fasinjojin ne a dai-dai Marabar Kankara da misalin karfe 9 na dare a ranar 22 ga watan Maris di da ya gabata.

LABARAI MASU ALAKA

Za’a fara rataye masu garkuwa da mutane a Katsina

An yi garkuwa da dan uwan gwamnan jihar Bauchi

Anyi garkuwa da ‘yan wasa biyu a Firimiyar Najeriya

Sakataren Gwamnatin jihar Mustapha Muhammad Inuwa ne ya bayyana hakan ga manema labarai lokacin da jami’an tsaron suka yi nasarar ceto wasu mata biyu cikin wadanda aka sace din.

Alhaji Mustapha yace za’a kai wadanda aka ceto din zuwa asibitin gidan Gwamnatin jihar don duba lafiyar su, kafin daga bisani kuma a mika su ga iyalan su.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!