Labarai
Masu hakar Kabari sun bukaci mahukunta da masu hali su kai wa Makabartu dauki

Kungiyar masu hakar Kabari ta jihar Kano, ta bukaci mahukunta da su kai wa makabartun jihar daukin gaggawa duba da irin mawuyacin halin da suke ciki.
Shugaban kungiyar Muhammadu Inuwa Umar ne ya bayyana hakan a zantawarsa da wakiliyarmu Hauwa’u Bello Abdullahi.
Muhammadu Inuwa Umar, ya kuma nemi daukin al’umma wajen tallafa musu da kayan aiki da za su rika yin amfani da su wajen gyara Makabartu don kare su daga lalacewa.
You must be logged in to post a comment Login