Labarai
Masu magungunan dabbobi su rinka hada kai da masana – Sarkin Kano
Mai martaba sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero, ya bukaci masu sayar da magungunan dabbobi da su rika hada kai da masana don yakar cututtuka da ke addabar dabbobi.
Sarkin na Kano ya bayyana hakan ne lokacin da ya ke karbar jami’an kungiyar masu sayar da magungunan dabbobi wadanda su ka kai masa ziyara fadarsa.
Alhaji Aminu Ado Bayero ya bayyana muhimmancin da sana’ar ke da shi musamman wajen tausayawa dabbobi don yakar cututtukan da ke damunsu.
Sarkin Kano Aminu Ado Bayero shi ne shugaban majalisar sarakuna – Ganduje
Yan jarida na da muhimmiyar gudummuwa wajen wanzar da zaman lafiya – Sarkin Kano
A nasa bangaren, shugaban kungiyar na jihar Kano Alhaji Abdullahi ADO Abubakar, ya ce, sun je fadar ta Kano ce da nufin neman tabarrakin sarkin da kuma sanarwa sarkin irin yadda suke gudanar da sana’arsu.
Wakilin mu na fadar Kano Muhammadu Harisu Kofar Nassarawa ya ruwaito cewa, Sarkin na Kano ya kuma karbi tawagar kungiyar mata masu taimakawa marayu ta jihar Kano, a karkashin shugabar kungiyar Hajiya Rukayya Abdurrahman, a fadarsa.
You must be logged in to post a comment Login