Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Sarkin Kano Aminu Ado Bayero shi ne  shugaban majalisar sarakuna – Ganduje

Published

on

Gwamnan Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya sanya hannu akan dokar da ya yiwa gyaran fuska ta masarautu inda ta tabbatar da Sarkin Kano Alhaji Aminu AdoBayero a matsayin  shugaban majalisar sarakuna maimakon tsarin karba-karba.

Gwamna Ganduje ya sanya hannun ne a yau ya yin taron majalisar zartarwa a fadar gwamnatin Kano

Ganduje ya Kara da cewa saboda muhimmancin Masaurautar Kano da take ta hudu a Nigeria wanda ba’a son samun yanayin da za’a hana ko dakatar da Sarkin na Kano shiga taron shugabannin hukumomin sarakuna na kasa, adon hakane a ka mayar da shugabancin na din -din akan sarkin Kano.

A cewar dokar ta kuma kara adadin masu zaben sarki daga mutum hudu zuwa mutum biyar.

Wakiliyar mu ta fadar gwamnatin Kano  Zahra’u Nasir ta ruwaito cewa a ya yin taron majalisar zartarwar an kuma sanya hannu akan dokar da ta bada damar kafa hukumar masu bunciken kayayyaki da kudade a dukkan ma’aikatun gwamnati.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!