Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Masu sana’ar ruwan kura na barazanar lalata titin Ƙofar Nasarawa – Dakta Kabiru Getso

Published

on

Ma’aikatar muhalli ta jihar Kano za ta ɗauki mataki kan masu ɗibar ruwan kura a ƙarƙashin gadar Ƙofar Nasarawa.

Kwamishinan muhalli Dakta Kabiru Ibrahim Getso ne ya bayyana hakan lokacin da ya kai zirar wajen a Asabar ɗin nan, a wani ɓangare na ranar tsaftar muhalli.

Getso ya ce “Mun samu ƙorafi kan yadda masu ɗiban ruwa a ƙarƙashin gadar ke barazanar lalata titun da aka kashe miliyoyin nairori wajen ginawa”.

“Mun ba su kwana uku su gyara wajen ko mu hana su ɗibar ruwan a wajen gaba ɗaya” in ji Getso.

Kwamishinan ya bayyana damuwar sa kan yadda masu sana’ar ɗiban ruwan suke barin ruwa yana kwaranya titin abinda ke barazana ga lalacewar sa.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!