Labarai
Mataimakin shugaban Majalisar Dattijai ya musanta rahoton bukatar sojoji su ceto kasar nan
Mataimakin shugaban Majalisar Dattijai Sanata Ike Ekweremadu ya musanta rahoton da aka yada da cewa ya bukaci Sojoji su ceto kasar nan daga halin da ta shiga.
Ekweremadu na fadin hakan ne a jiya Lahadi a garin Yenagoa na Jihar Bayelsa yayin taron kwamitin zartaswa na ‘yan Majalisar kasashen rainon Ingila shiyyar Afirka karo na 74, wanda gwamnan Jihar ta Bayelsa Seriake Dickson ya kasance mai masaukin baki.
Cikin wata sanarwa da mai Magana da yawunsa Uche Anichukwu ya bayar, ya ce an juya jawabin da Ekweremadu ya gabatar a zauren Majalisar Dattijan, bayan da ya bayyana irin girmamawar da ya ke yi wa Rundunar Sojin kasar nan.
A cikin jawabin na sa ya bukaci ‘yan Majalisar su kasance masu taka tsan-tsan tare da baiwa Dimokradiyya kariya, yayin gudanar da harkokinsu na siyasa domin kaucewa fadawa cikin kura-karen da ‘yan siyasar baya suka tafka da suka yi sanadiyyar juyin mulki.
Sanata Ike Ekweremadu ya musanta cewa jawabansa ba wai suna nufin fatann juyin mulki daga Sojoji ba.