Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Mataimakin shugaban Majalisar Wakilai ya yi korafi kan uwar jam’iyyar APC

Published

on

Mataimakin shugaban Majalisar Wakilai Ahmed Idris Wase, ya gabatar da korafi a kan matakin uwar jam’iyyarsu ta APC, bisa raba muƙaman shugabannin majalisa ta goma ga shiyyoyin Nijeriya.

Ahmed Idris Wase, tare da wasu masu neman shugabancin Majalisar ta wakilai, sun kai takardar korafin ne shalkwatar APC ta kasa da ke birnin tarayya Abuja.

Ta cikin takardar korafin nasu, sun bukaci jam’iyyar ta sake yin nazari kan matsayarta.

 

Mataimakin shugaban, ya bayyana haka ne lokacin da yake zantawa da manema labarai a shalkwatar jam’iyyar ta APC, jim kaɗan bayan miƙa takardar ƙorafinsu ga shugabancin jam’iyyar game da matakin da ta ɗauka.

Matakin nasu na zuwa ne a lokacin da kwamitin gudanarwa na jam’iyyar ke gudanar da wani taron gaggawa a kan rikicin da ya taso game da batun shugabancin majalisa ta 10.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!