Labarai
Matakan Gwamnatoci sun kasafta fiye da biliyan 600
Gwamnatin tarayya da jihohi da kananan hukumomi sun kasafta naira biliyan dari shida da casa’in da uku da miliyan dari biyar da ashirin da tara a matsayin kasonsu na rabon arzikin kasa na watan Satumba.
Hakan na kunshe ne cikin wata takardar bayan taro kwamitin rabon arzikin kasa, mai dauke da sa hannun akanta janar na tarayya Ahmed Idris.
Rahotanni sun ce kudaden sun gaza na watan shekaran jiya jiya na Agusta wanda aka raba naira biliyan dari shida da talatin da daya da miliyan dari bakwai da casa’in da shida.
Kididdigar rabon ya nuna cewa, gwamnatin tarayya ta karbi naira biliyan dari biyu da casa’in da uku da miliyan dari takwas da daya, jihohi sun samu naira biliyan dari da tamanin da shida da miliyan dari takwas da goma sha shida yayin da kananan hukumomi su ka karbi naira biliyan dari da arba’in da miliyan dari takwas da sittin da hudu.
Sai jihohin yankin Niger Delta wadanda suka karbi kaso goma sha ukunsu da ya kai naira biliyan hamsin da daya da miliyan dari biyar da talatin da biyu sai kuma hukumomin da ke tattara haraji wadanda suka karbi kasonsu da ya kai naira biliyan ashirin da miliyan dari biyar da goma sha bakwai.