Connect with us

Labarai

Matar da ta haifi jarirai 5 a Kano ta rasu

Published

on

An gudanar da janaizar Marigayi Hafsat Yusif, wadda ta haifi jarirai biyar jiya Laraba a Asibitin kwararu na Murtala Muhammad a nan Kano.

Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Kano ta ce, mahaifiyar yan biyar din Malama Hafsat Yusif, ta rasu ne sakamakon zubar jini duk da kokarin da jami’an lafiya suka yi wajen ceto rayuwarta kamar yadda jami’in yada labarai na ma’aikatar Nabulisi Abubakar Kofar Naisa, ya shaida wa wakilinmu Abba Isah Muhammad.

Malam Salisu Nafi’u, Shi ne mijin marigayya ya bayyana cewar, yanzu haka sun gudanar da jana’izar marigayar a Unguwar hotoro Ladanai da ke nan Kano.

A zantawar marigayya Hafsat Yusif, da manema labarai a jiya Laraba bayan haihuwarta, ta bayana wasu cikin burinta idan Allah ya rayata da yayan nata, inda ta ce, tana so su samu damar yin karatu mai zurfi.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!