Connect with us

Labarai

Ma’aikatan jihar Adamawa sun yi zanga-zanga kan kin biyan albashi

Published

on

Wasu ma’aikata a jihar Adamawa, sun yi zanga zangar lumana, game da rashin biyansu albashinsu na kusan watanni shida.

Su dai ma’aikatan maza da mata, na daga cikin ma’aikatan da tsohuwar gwamnatin APC ta Sanata Muhammadu Bindo Jibrilla ta dauka aiki, a shekarar 2018.

Tun shigowarta, gwamnatin PDP ta Ahmadu Umaru Fintiri, ta dakatar da wadanan  ma’aikata bisa dalilan cewa sai ta gudanar da bincike.

Gwamnatin ta kafa kwamitocin binciken ma’aikatan, wanda kawo yanzu ba a fayyace ma su makomarsu ba.

Da yake tarbar ma’aikatan, mataimakin gwamnan jihar Adamawan Chief Crowther Seth, ya bukace su da su kwantar da hankulansu inda ya ce gwamnati za ta sake duba lamarinsu da idon rahama.

Kawo yanzu kungiyar kwadago ta NLC a jihar ba ta ce komi ba yayin da wasu ma’aikatan ke cikin halin ni ‘yasu sanadiyyar rashin biyansu albashin.

 

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 332,922 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!