Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Kano

Mayar da almajirai jihohinsu abu ne mai kyau- Youths Helping Hand

Published

on

Wata kungiyar ci gaban matasa tare da tallafawa mabuka mai suna Youths Helping ta nuna jin dadinta dangane da yadda gwamnatin jihar Kano ta mayar da almajirai jihohinsu na asali a wani bangare na matakan kare yaduwar annobar Covid-19.

Shugaban kungiyar Jibril Nasir Mu’azu ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da kungiyar ta fitar aka rabawa manema labarai a Kano.

Sanarwar mai dauke da sa hannun sakataren yada labaran kungiyar Aminu Yusuf Aliyu ta ce matakin da gwamnatin ta dauka abin a yaba ne duba da irin matsalar da barin almajirai suna yawo a gari zai haifar, a yayin da adadin masu dauke da cutar Corona ke kara yaduwa a arewacin kasar nan.

Shugaban kungiyar ta Youths Helping Hands Jibril Nasir Mu’azu ya kuma yi Kira ga al’umma da su ci gaba da daukar matakan kariya tare da bin shawarwarin masana harkokin lafiya.

A watan da ya gabata ne, gwamnonin jihohin arewa suka tabbatar da rushe tsarin almajiranci inda suka bayar da umarnin mayar da almajirai jihohinsu na asali.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!