Labarai
Mazauna Kontagora da wasu yankuna a Jihar Neja sun gudanar da addu’o’in neman ɗaukin Ubangiji kan hare-haren ‘Yan bindiga

Mazauna yankunan Neja ta Arewa sun gudanar da taron addu’a ta musamman a filin Idin Kontagora, hedikwatar karamar hukumar Kontagora, domin neman taimakon Allah kan yawan hare-haren ‘yan bindiga da suka addabi al’ummomin manoma a yankin.
Yankunan da abin ya fi shafa sun haɗa da Magama, Mariga, Rijau, Borgu, Kontagora da Mashegu, inda hare-haren suka ƙaru a makonni kalilan da suka gabata, lamarin da ya tilasta wa daruruwan mazauna, musamman mata da yara, barin gidajensu domin tsira da rayukansu.
Wannan matsanancin hali ne ya sa jama’ar yankin suka nemi mafita ta hanyar addu’a domin neman sauƙi daga wannan matsalar tsaro da ta daɗe tana damunsu.
Wani daga cikin mutanen da suka rasa matsugunansu, wanda bai so a bayyana sunansa ba, ya shaida wa Daily Trust cewa ɗaruruwan musulmi daga yankunan da abin ya shafa – ciki har da Kontagora, Mashegu, Rijau da Magama – sun halarci taron addu’a.
You must be logged in to post a comment Login