Connect with us

Labaran Wasanni

Mbappe ya tafi jinyar rauni na mako uku

Published

on

Dan wasan gaban kungiyar Kwallon kafa ta Paris Saint German (PSG), ta bayyana cewar dan wasanta Kylian Mbappe zai shafe sati uku yana jinyar raunin da ya samu.

Tafiya jinyar da dan wasan zai yi , ta sa ba zai samu damar buga wasan da tawagar sa zatayi da da Atlanta ta kasar Italiya ba a gasar cin kofin Zakarun Turai na Champions league , ranar 12 ga watan Augusta, a wasan dab da na kusa da na karshe wato Quarter Final.

Dan wasan ya samu rauni a idon sawun sa (Ankle ) bayan da sukayi arangama da dan wasan Saint Etienne Perin, a wasan karshe na Coupe de France , da PSG ta samu nasara da ci 1 da nema.

Tafiya, jinyar dan wasan ta kawo tasgaro a kokarin da kungiyar take na daukar kofin Zakarun turai , wanda yake daga gaba -gaba a burin kungiyar .

Mbappe , ya zura kwallaye 30 a gasa daban -daban daya bugawa PSG a Bana, kafin a baiwa tawagar nasarar lashe kofin kasar Faransa na Ligue 1, bayan dakatar da gasar sakamakon Annobar Corona.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 330,179 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!