Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Me ya ke faruwa da Kwankwasiyya a Kano ta Kudu?

Published

on

Da alama ɓaraka ta kunno a tafiyar NNPP Kwankwasiyya daga yankin Kano ta kudu bayan fitar wasu kalamai na Ɗan Majalisar Tarayya na Rano, Kibiya da Bunkure Alhaji Kabiru Alhassan Rurum.

A cikin wani bidiyonsa da ya karaɗe kafafen sada zumunta ya nuna shi yana barranta kansa daga matakin da Gwamnatin jihar ta ɗauka game da sha’anin Masarautu.

 

Kawu Sumaila da neman a samar jihar Tiga

A yan makonnin da suka wuce Sanatan Kano ta Kudu Alhaji Abdurrahman Kawu Sumaila ya gabatar da kudurin neman samar da jihar Tiga daga Kano, wanda zai kunshi yankin Kano ta Kudu.

Wannan lamari ya janyo wa Kawu Sumaila samun tirjiya daga magoya bayan Kwankwasiyya inda suka rika mayar da martani musamman a kafafen sada zumunta.

Sai dai a wani bidiyon an hango Sanata Kawu yana ta yabon Jagoran Kwankwasiyya Engr. Rabi’u Musa Kwankwaso kan halaccin da ya yi masa har ya samu takara.

 

Shin Kudirin Kawu da Kalaman Rurum suna da alaka?

Wasu dai na ganin cewa ci gaba da maganar samar da jihar Tiga da Kawu ya yi da kuma kalaman Rurum na nuna wa Duniya cewa da alama sun soma hada kayansu domin tsallaka layi daga Kwankwasiyya.

Amma wasu na ganin a’a ba komai ba ne wannan, sai kawai nuna damuwarsu kan matakin da bai masu daɗi ba a tafiyar Gwamnatin Kano.

 

Ko Alhassan Ado Doguwa ya soma sharewa Kawu da Rurum hanya ne?

A wani bidiyonsa da ya yi yawo a Social Media, Dan Majalisar Tarayya na Tudunwada da Doguwa Alh. Alhassan Ado Doguwa ya fito fili ya nuna cewar, faduwar APC a zaben Gwamna na shekarar 2023 yana da alaka da ficewar Kawu da Rurum daga jam’iyyar.

Doguwa ya jinjina girmansu tare da koɗa su yana fadar muhimmanci da amfaninsu ga tafiyar APC, domin ya nuna da suna jam’iyyar babu ta yadda za a yi Kwankwasiyya ta kai labari.

 

Ko APC na zawarcin Kawu da Rurum?

Rahotonnin sirri da Freedom Radio ta samu sun nuna cewa tabbas APC na zawarcin Sanata Kawu Sumaila da Kabiru Alhassan Rurum har ma wata majiyar ta ce, suna da shirin komawa amma ba sa son komawa ƙarƙashin jagorancin tsohon Gwamna Dr. Abdullahi Umar Ganduje.

Wasu kuma suna ganin cewa bidiyon Alhassan Ado Doguwa tamkar sharar hanya ne tare da sake fitowa da Duniya cewa akwai wata a ƙasa.

 

Kalaman Rurum sun hargitsa ƴan Kwankwasiyya

Babu shakka kalaman Alh. Kabiru Alhassan Rurum sun fusata magoya bayan Kwankwasiyya la’akari da martanin da ya ke samu har kawo yanzu a kafafen yaɗa labarai da kafafen sada zumunta.

 

Wane tsokaci kuke da shi kan wannan sharhi? Ku a jiye mana akwatin sakon da ke ƙasa.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!