Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Me yake faruwa da Rarara?

Published

on

Da alama dangantaka ta ƙara yin tsami tsakanin mawaƙin APC Dauda Kahutu Rarara da Gwamnatin Kano.

A baya dai tuni mawaƙin ya ayyana cewa ba zai yi jam’iyyar APC a Kano, har ma ya rungumo ADC ta Sha’aban Sharaɗa.
Sai dai yanzu haka an wayi gari da zazzafan martani tsakanin mabiyan Rarara da magoya bayan Gwamnatin Kano.

Hakan ya biyo bayan wata sabuwar waƙa da Rararan ya fitar kan ɗan takarar APC Bola Ahmad Tinubu.

A cikin waƙar mawaƙin yayi gugar zana da habaice-habaice wanda ba a tantance dawa yake ba.

Ga kaɗan daga ciki.

•Kace a cire sunana wannan na ji

•Dama ban ce a saka ni ba inda kaji

•Duk wani taro da kake kaina to na ji

•Mu harkar Tinubu ba sai da takarda ba•Shi dai zabo a sanina baya cara

•Ko a buga ko a bari dai nine Rarara

Na ari rigar gamji ko dan nayi sara

•In Dutse ya kafu ba dai turewa ba.

Magoya bayan Gwamnatin Kano da dama ne dai suka yi martani musamman a shafukan Facebook.

Ciki har da shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa Auwal Lawan Shu’aibu Aranposu.

Wanda ya ce
“Zamu saka Manjagara, Mu yage Hakoran mutum, wargi fa waje yake samu”.

Wasu bayanai da Freedom Radio ta samu sun nuna cewa ɓarakar na ƙara zafafa ne kan shirye-shiryen zuwa Bola Ahmad Tinubu Kano wanda kowane ɓangaren ke ganin yana da ruwa da tsaki.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!