Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Wasanni

Messi ya ci gaba da karbar horo a Barcelona

Published

on

Zakakurin dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Barcelona, Lionel Messi, ya dawo sansanin kungiyar domin ci gaba da daukar horo, bayan gaza cimma burin sa na ficewa daga kungiyar.

Messi, mai shekaru 33, ya dai nemi amincewar Barcelona kan aniyar sa ta barin kungiyar a ranar 25 ga watan jiya, lamarin da ya janyo sa-in-sa a duniyar wasan kwallon kafa.

Dan wasan ya kuma yanke hukuncin ci gaba da zama a kungiyar ta Barcelona a ranar Juma’ar makon jiya, bayan da hakar sa ta gaza cimma ruwa.

Wannan shine karo na farko da Messi zai yi atisaye tare da sabon mai horas da kungiyar Ronald Koeman.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!