Labarai
Ministan kasafi:Ana sa ran tattalin arzikin Najeriya zai karu da sama da kashi 3
Ministan kasafin kudi da tsare-tsare na Najeriya, Udoma Udo Udoma ya ce, akwai yiwuwar tattalin arzikin kasar zai karu da fiye da kashi uku a bana kamar yanda wani rahoton Asusun bayar da lamuni na duniya, IMF ya fitar.
Udo Udoma ya ce rahoton da IMF ya fitar Ya bayyana yanda tattalin arzikin kasar nan a watan junairun da ya gabata ya yi sama musamman ta bangaren kasuwar danyen mai ya karu da sama da Kashi biyu.
Udoma ya kara da cewa Ana saran kasafin kudin bana zai habaka tattalin arzikin kasar nan tare da samarwa matasan ayyukan yi a kasar nan, baya ga ragewa da yawa daga cikin al’umma halin matsin da suke ciki.
A cewar Minista Udo udoma a dadin da ake sa ran za’a samu ya kai sama da kaso tara a shekarar nan, daga cikin kaso goma sha daya hkamar yadda yake a karshen shekarar 2018.