Labaran Kano
Minzali Danbazau: An tallafawa mata sama da 100 da jari a Kano
Gidauniyar Munzali Danbazau Foundation ta koyar da mata sama da 100 sana’o’in dogaro da kai da kuma basu jari domin yin sana’o’in
An tallafawa matan ƙaramar hukumar birni da suka fito daga dukkan mazaɓun ƙaramar hukumar domin anfanar da yankin
Shugaban gidauniyar Alhaji Minzali Abubakar Danbazau ya ce la’akari da yadda ake samin rashin sana’o’in ga mata yasa wannan gidauniyar tayi huɓɓasa wajen ganin ta tallafawa mata domin suma su sami hanyar dogaro da kai
Allah Minzali Danbazau ya kuma ce wannan wata ɗanba ce suka ɗaura wajen shiga lunguna da saƙo na yankin nasu domin tallafa mabuƙata
Da yake jawabi yayi bayar da tallafin ɗan majalisar jiha na ƙaramar hukumar Birni Sarki Aliyu Daneji cewa yayi samin irin wannan gidauniyar a cikin yankuna zata taimaka wajen rege matsin rayuwa musamman ga mata
Sarki Aliyu Daneji ya kuma buƙaci sauran ƙungiyoyi da su ci gaba da tallafawa al’umma da hanyoyin da zasuyi koyi sana’o’in dogaro da kai kamar yadda wannan gidauniyar ta Minzali Danbazau Foundation tayi
Daga ƙarshe gidauniyar Munzali Danbazau Foundation tace zata ci gaba da koyar da mata sana’o’in dogaro da kai ba iya wannan kawai da akayi ba
You must be logged in to post a comment Login