Ƙetare
Mojtaba Khamenei ya zama sabon jagoran addinin ƙasar Iran

Mojtaba Khamenei ya zama sabon jagoran addinin ƙasar Iran, bayan da majalisar ƙwararrun ƙasar ta zaɓe shi domin ya gaji mahaifinsa Ayatollah Ali Khamenei.
Gidan talabijin na gwamnatin Iran ne ya sanar da hakan, inda aka ce duk da halin yaƙi da kuma hare-haren da aka kai ofisoshin majalisar, wanda ya yi sanadin mutuwar wasu mambobinta da jami’an tsaro, majalisar ba ta dakata ba wajen gudanar da zaɓen sabon jagoran tsarin Musulunci.
Sanarwar ta ce majalisar ta tabbatar da naɗin Mojtaba Khamenei a matsayin jagoran addinin ƙasar, lamarin da ya sa ya zama jagora na uku a tarihin Iran, kuma na farko da ya gaji mahaifinsa.
Rahotanni sun ce an daɗe ana hasashen Mojtaba zai gaji mahaifinsa tun bayan da aka kashe Ali Khamenei a harin da Amurka da Isra’ila suka kai.
An haifi Mojtaba Khamenei a ranar 8 ga watan Satumban 1969 a birnin Mashhad, kuma shi ne na biyu cikin ’ya’yan Ali Khamenei shida.
You must be logged in to post a comment Login