Kasuwanci
Mu na fuskantar barazana a rayuwar mu – Masu sana’ar Danja
Masu gudanar da sana’a a kan danjar titi sun koka bisa yadda suke fuskantar barazana ga lafiyar su har ma rayuwakn su.
A zantawar mu da Mustaph Sa’idu Muhd wanda guda ne daga cikin masu yin sana’ar a kan danja ta Ɗan agundi ya shaida cewa “ A kullum muna muna fsukantar barazanar haɗarin ababen hawa, sakamakon yadda sana’ar mu ta ke a kan titi, kuma ababuwan hawa muke bi muna yin tallan”.
“sai dai mun gwammace muyi wannan sana’a da muje mu yi zaman banza duk don mu rufawa kan mu asiri, amma duk ƙoƙarin da muke muna kula da tsaro a wajen sana’ar mu ta hanyar tabbatar da ba a samu wani abu mai kama da satar waya ko guduwa da canjin masu ababen hawa ba.
“A cikin sana’ar nan na yi makarantar sakandire na shiga kwaleji yanzu haka, kuma da ita nake dukkanin al’amuran rayuwa ta”.Sabi’u Ona shi ne shugaban ƙungiyar masu sana’ar danja a Ɗan agundi ya bayyana cewa “Wannan sana’ar ta mu Sana’a ce mai muhimmanci, saboda kowacce kasuwa zaka je a Kano sai katarar da masu irin Sana’ar mu, saboda yadda matasa a yanzu ba su da aikin yi”.
You must be logged in to post a comment Login