Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

KannyWood

Muhimman abubuwan da suka faru a Kannywood cikin makon da ya gabata

Published

on

A ranar Asabar ne aka rintsar da sabbin shuwagabannin ƙungiyar masu shirya finafinan Kannywood ta Nijeriya, wato MOPPAN, biyo bayan zaben da aka gudanar a garin Dutse babban birnin jihar Jigawa.

Tsohon shugaban Hukumar Tace Finafinai ta Ƙasa (NFVCB) shiyyar arewa-maso-yammacin ƙasar nan, Dakta Ahmad Sarari, shi ne ya lashe zaɓen zama shugaban kungiyar ta MOPPAN inda yayi nasarar kan abokin takararsa kuma shugaban ƙungiyar da ya nemi yin ta-zarce, wato Alh. Abdullahi Maikano Usman, Wanda tuni ya aike da sakon taya murna ga sabon shugaban.

Dakta Sarari dai yayi alkawarin sake bunkasa kasuwar fina-finan Hausa da kuma kara fadada tasirin masana’antar zuwa sauran jihohi, sannan yayi alkawarin ganin ya magance dukkan matsalolin dake addabar masana’antar ta Kannywood.

Dakta Ahmad Sarari Sabon Shugaban Kungiyar Moppon

A wani labarin kuma Wasu ɗalibai ‘yan Arewacin Najeriya da ke karatu a ƙasar Indiya da malaman su Indiyawa sun karrama jarumi Ali Nuhu da lambar yabo, kamar yadda ya shaidawa BBC cewa sun gayyace shi har zuwa can kasar ta India inda suka karramashi a yayin gudanar da bikin ranar al’adu.

Yayin da ake karrama jarumi Ali Nuhu a kasar India.

A wani bangaren kuwa juruma Hafsat Idris wadda aka fi sani da Barauniya ta fashe da kuka a yayin da tsohon sanata mai wakiltar Kaduna ta tsakiya sanata Shehu Sani ke bata kyautar Face of Kannywood da ta lashe a gasar City Movie Award ta bana da aka gabatar a birnin Lagos.

Tun da farko dai Jarumar ta rufe fuskarta yayin da yake bata kyautar, inda bayan da ta karba aka mika mata abin Magana kawai sai ta rushe da kuka tana mai godiya bisa karramawar da aka yi mata.

Wannan batu dai ya dauki hankulan masoyanta da dama, inda suka rika bayyana mabambamtan ra’ayoyi kan hakan a shafukan sada zumunta.

Jaruma Hafsat Idris jim kadan bayan ta karbi kyautar.

Kotun majistret Mai lamba 15 karkashin Mai sharia Muntari Garba Dandago ta bada belin jarumar nan da tayi fice a kafafan sada zumunta wato Sadiya Haruna.

Mai Sharia Dandago ya ayyana cewar laifin da ake zargin Sadiyar ta aikata laifi ne da za’a iya bayar da ita beli.

Don haka ya bayar da belin bisa sharadin mutum biyu da zasu tsaya mata idan kuma ta tsere to wadanda suka karbi belin za su biya zunuzurutun kudu har naira dubu dari biyar.

Kotun ta kuma yi hani ga Sadiyar da mai kara Isa A Isa kan kada wanda ya kara yin maganar a wata kafar sadarwa ko wacce iri ce har zuwa karshen shariar.

Tun da farko dai ‘yansanda ne suka gurfanar da sadiyar a gaban kotun sakamakon korafin da jarumi Isa A. Isa ya shigar na zargin ta bata masa suna wanda ita kuma Sadiyar ta musanta zargin.

Wakilin mu Yusuf Nadabo Isma’il ya ruwaito cewar an dage shari’ar zuwa ranar 14 ga watan gobe.

Hoton jarumi Isa A. Isa da Sadiya Haruna.

A dai masana’antar ta Kannywood a wannan makon da muke ciki ne Fitaccen mai bada umarni Al’amin Chiroma da mai dakinsa Wasila Isma’il suka cika shekaru 17 da yin aure.

Al’umma da dama nata fatan alkhairi ga wannan iyali.

Hoton jarumi Al’amin Chiroma da mai dakinsa.

Jarumi Mustapha Naburaska ya kammala ginin gidansa a wannan makon da muke bankwana dashi a Kano kamar yadda mujallar Film Magazine ta rawaito, tuni masoya suke ta taya jarumin murna.

Hoton sabon gidan jarumi Mustapha Naburaska.

Ku bayyana mana ra’ayoyin ku game da wadannan labaran.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!