Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Mun bai wa rundunar sojin Najeriya naira tiriliyan daya cikin shekaru 2 – Zainab Ahmed

Published

on

Ministar kudi kasafi da tsare-tsare Zainab Ahmad, ta ce, ma’akatarta ta bai wa rundunar sojin kasar nan jimillar sama da naira tiriliyan daya tsakanin watan Janairun shekarar 2019 zuwa Afrilun wannan shekara.

 

Hajiya Zainab Ahmed ta bayyana hakan ne lokacin da ta gurfana gaban kwamitin kula da rundunar sojin kasar nan na majalisar dattijai.

 

Tun farko dai kwamitin kula da harkokin soji na majalisar ya gayyaci ministar ce sakamakon korafin da sojin kasar nan su ka yi na cewa suna bin ma’aikatar bashin naira biliyan hamsin da ya kamata a basu don ci gaba da ayyukan da suke yi na yaki da ta’addanci

 

Sai dai ministar ta ce rundunar sojin ta karbi isassun kudade daga ma’aikatar da zai biya bukatunsu.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!