Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Mun biya diyya ga iyalan tsoffin ma’aikatan mu da suka rasu – NDLEA

Published

on

Hukumar yaƙi da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta ƙasa NDLEA ta ce, ta biya diyyar sama da naira miliyan 163 da dubu dari hudu ga iyalan wadanda suka rasu a bakin aiki su 188.

Shugaban hukumar Birgediya janar Muhammad Buba Marwa mai ritaya ne ya bayyana hakan lokacin da yake miƙa chakin kudi ga wasu iyalai 14 na mamatan.

Ya ce, waɗanda suka samu kuɗaɗen sun rasa mazajen su ne tun a shekarar 2014, kuma tuni mafi yawa daga cikin iyalan, suka fara ganin kuɗin ta asusun su.

Buba Marwa ya yabawa shugaban ƙasa Muhammadu Buhari bisa goyon bayan da ya bai wa hukumar, na biyan diyya ga iyalan waɗanda suka rasa rayukan su a bakin aiki don rage musu raɗaɗi.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!