Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Kasuwanci

Zamu hukunta duk wanda ya saba dokar canjin kudaden ketare – CBN

Published

on

Bankuna sun ce duk wanda ya sabawa sabuwar dokar canjin kudaden kasashen ketare zai fuskantar tsatstsauran hukunci daga Babban Bankin Najeriya CBN.

Bankunan sun bayyana hakan ne ta cikin sakonnin karta kwana da suka aike wa abokanan kasuwancinsu.

“Dangane da manufar CBN na inganta hanyoyin musayar kudaden waje don gudanar da halattattun hada-hada, mun sha alwashin samar muku da canjin kudaden don tafiye-tafiye da kasuwanci tare da biyan kudin makaranta a kasashen na ketare da sauran ma’amaloli,” in ji su.

Bankunan sun kuma yi kira ga abokanan kasuwancin na su dasu bada hadin kai wajen cimma nasarrorin manufar sabon tsarin samar da canjin kudaden don kiyaye fushin doka.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!