Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Mun ceci rayukan mutane 101 daga ibtila’in gobara a watan satumba

Published

on

Hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta ceci rayukan mutane 101 da dukiyoyin da suka kai Naira miliyan 21 daga ibtila’in gobarar da aka samu sau 21 a watan Satumba.

Mai magana da yawun hukumar Saminu Abdullahi, ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar ranar litinin a Kano, inda ya ce hukumar ta samu kiran gaggawa sau 77 da kuma kiran karya sau 11 a tashoshin kashe gobara 27.

Ya kara da cewa rayuka takwas sun salwanta sannan dukiyoyi kimanin Naira miliyan 7 da dubu 300 sun kone kurmus a cikin watan na satumba lokaci.

Abdullahi ya kuma shawarci al’umma da su rinka kula wajen yin amfani da wuta a koda yaushe don kaucewa afkuwar hatsari a nan gaba.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!