Labarai
Mun dakatar da shirin fara karɓar harajin kaso 15 cikin 100 kan fetur- NMDPRA

Hukumar kula da harkokin man fetur ta Najeriya NMDPRA ta ce, ta dakatar da shirin fara karɓar harajin kaso 15 cikin 100 kan albarkatun man fetur ɗin da ake shigaar da su Najeriya daga ƙasashen ketare.
Mai magana da yawun hukumar ta NMDPRA George Ene-Ita, ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar yau Alhamis inda ya bukaci al’umma da su daina fargaba.
A baya dai a ranar 29 ga watan Oktoba shugaban Ƙasa Bola Tinubu, ya amince da saka harajin kan man fetur da Man Dizel, wanda zai ƙara farashin man da ake saukewa a defo-defo, kuma ɗaya daga cikin manufarta shi ne ƙarfafa matatun mai na cikin gida.
Gwamnatin tarayya ta ce da ta tsara fara aiki da harajin ne daga ranar 21 ga watan Nuwamban nan, kafin matakin tsaida amfani dashi da ta sanar.
You must be logged in to post a comment Login