Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Mun fara raba sabbin kudin Naira a bankuna – CBN

Published

on

Babban bankin kasa CBN ya ce, sabbin takardun kudi na Naira da aka yi wa gyaran fuska tuni sun isa bankuna domin fara amfani da su.

Gwamnan babban bankin Godwin Emefiele ne ya sanar da hakan a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Twitte.

Rubutun nasa na zuwa ne bayan ziyarar da ya kai wa shugaban kasa Muhanmadu Buhari a Daura domin yi masa karin bayani kan sake fasalin kudin Naira da kuma manufar dokar takaita kudi da aka samar.

Ya ce, sake fasalin kudin da kuma dawo da manufofin takaita kudin an yi su ne ba don tsanantawa al’umma ba sai don ci gaban tattalin arzikin Najeriya.

Emefiele ya kuma bukaci ‘yan Najeriya da su rungumi hanyoyin sadarwa na zamani da ake amfani da su wajen hada-hadar banki da hada-hadar kudi a Najeriya.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!