Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Wata Sabuwa: KAROTA za ta ci gaba da kamen masu goyo a babur

Published

on

Hukumar KAROTA ta ce, zata ci gaba da kamen masu yin goyo a babur mai ƙafa biyu a Kano.

Shugaban hukumar Baffa Babba Ɗanagundi ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai da ya kira a ranar Talata.

Baffa ya ce, a baya Acaɓa aka hana ba goyo ba, amma yanzu doka ta haramta yin goyo ƙarara a babur.

Dama dai an sha kai ruwa rana tsakanin ƴan KAROTA da jama’a kan dokar goyon.

Kotu ma ta taɓa hana hukumar kama masu goyo bayan da wasu lauyoyin al’umma suka shigar da ƙara.

Sai dai a jawabin Baffa Babba ya ce, a baya magana ce ta Acaba shi yasa basu tsananta ba.

Wannan na zuwa ne, ƙasa da yini guda bayan da hukumar ta sanar da dokar hana masu baburan adadaita sahu bin manyan titunan jihar.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!