Connect with us

Labarai

Za mu ci gaba da tallafawa marayu – Inuwar marayu

Published

on

Inuwar Marayu da gajiyayyu ta Tudun Maliki, ta sha alwashin ci gaba da tallafawa ‘yaran da iyayen su suka rasu da iyayen da aka barsu da marayu da tallafin kayan abinci da kula da lafiyar su da Ilimin su.

Shugaban kungiyar Alhaji, Abdulkadir Kabiru Bayero, ne ya bayyana hakan ta bakin, mai magana da yawun kungiyar Malam Mustafha Karaye Ibrahim, yayin rabon tallafin kayan abinci na garin masara da Taliya da gidauniyar tallafawa al’umma ta Dangote ta baiwa kungiyar don Tallafawa marayu da gajiyayyun dake yankin unguwar ta Tudin Maliki.

Malam Mustapha Karaye Ibrahim, ya kuma ja hankalin masu hannu da shuni da daidaikun mutane wajen tallafawa wadan da basu dashi.

Wasu daga cikin ‘iyayan marayun da suka amfana da tallafin kayan Abincin da kamfanin na Dangote ya bayar don rabawa a karkashin kungiyar ta Inuwar Marayu da gajiyayyu dake Tudin Maliki sun bayyana farin cikin su da samun tallafin inda suka ce tallafin ya zo adaidai lokacin da ake bukatar sa.

Wakilin mu Abubakar Tijjani Rabi’u ya rawaito cewa, gidajen marayu 178 ne za su amfana da tallafin kayan abincin da gidauniyar ta Dangote ta bayar a unguwar ta Tudin Maliki.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 334,958 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!