Labaran Kano
Ya zama wajibi dalibai su jajirce don neman ilimi – Jami’ar Maryam Abacha
Jami’ar Maryam Abacha dake Maradi Dakta Bala Muhammad Tukur ya yi kira ga dalibai dake karatu a jami’o’i da su mai da hankali kan karatun su don su zama al’ummar da za’ yi alfahari dasu a kasar nan.
Daraktan hadin gwiwa da kulla alaka na Jami’ar Maryam Abacha Dake Maradi, Dakta Bala Muhammad Tukur ne ya bayyana hakan jim kadan bayan kammala shirin barka da hantsi na nan gidan radio freedom da ya gudana a safiyar yau.
Bala Muhammad yace yana da kyau iyayen dalibai su kara zage dantse wajan biyan kudaden makarantar ‘’ya’yan su, wanda da shi ne jami’ar ke gudanar da harkokin koyo da koyar wa.
An bukaci a daga darajar kwalejin ilimi ta Nasiru Kabara zuwa jami’a
Dokar kafa hukumar bunkasa ilimi na jihar Kano ya tsallake karatu na 2
Gwamnatin kano za ta kafa hukumar cigaban ilimi
Dakta Bala Muhammad ya kuma ce jami’ar a yanzu haka zata cigaba da wasu kwasa-kwasan da ta dakatar domin ganin an bunkasa harkar koyarwa dan ci gaban daliban jami’ar.
Daraktan ya kuma ce babban abin jin dadin shine daliban dake karatu a jami’ar sun fito ne daga kasar nan duk da cewa a jamhuriyar Nijar take.