Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

KannyWood

Mun Haramta haska fim da aka nuna yadda ake garkuwa da mutane – Afakallah

Published

on

Hukumar tace fina-finai da ɗab’i ta jihar Kano ta haramta haska duk wasu fina-finai da aka nuna yin garkuwa da mutane.

Hukumar ta ce, ta haramta nuna fim da haska yadda ake sayar da ƙwayoyi ko kuma shan kwayoyin maye.

Shugaban hukumar Alhaji Isma’ila Na’abba Afakalla ne ya bayyana haka, zantawar sa da Freedom Rediyo.

“Duk Film ɗin da aka nuna yadda ake kwacen waya a hannun mace, ko namiji ko wata mummunar ɗabi’a, shi ma ba za mu amince a haska shi ba”.

Afakallah ya kuma bukaci ƴan jarida da su taimakawa hukumar wajan wayar da kan al’umma domin dakile irin waɗannan matsaloli da aka iya gurɓata tarbiyyar matasa da ci gaban Rayuwar su.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!