Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Mun kama tsohon soja da laifin sayar da miyagun ƙwayoyi – NDLEA

Published

on

Hukumar yaƙi da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta ƙasa NDLEA ta cafke wani tsohon soja mai shekaru 96 da laifin sayar da miyagun ƙwayoyi a jihar Neja.

Hukumar ta ce, ta kama dattijon mai suna Pa Joseph ne a gidan sa da ke Rafin Sanyi a Suleja.

Wannan na cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar mai dauke da sa hannun mai magana da yawun ta Femi Baba Femi.

Sanarwar ta ce, bayan samun bayanan sirri, hukumar ta kai sumame gidan sa, kuma ta same shi da ƙwayoyin kimanin kilo uku.

NDLEA ta ce, a binciken da ta yi ta gano cewa tsohon sojan ya zabi yin sana’ar sayar da miyagun ƙwayoyin ne tun bayan da ya yi ritaya a shekarar 1982.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!