Labarai
Mun karɓi ƙorafi kan neman bincikar tsohon DIG Dasuki Galadanci- ICPC

Hukumar yaki da cin Hanci da Rashawa ta Najeriya ICPC ta karɓi takardar ƙorafi da ke neman a gudanar da cikakken bincike kan tsohon Mataimakin Sufeto Janar na ’Yan Sanda, Dasuki Galadanci, bisa zargin mallakar kadarorin da darajarsu ta kai biliyoyin naira, waɗanda ake zargin sun wuce abin da zai iya samu ta hanyar sahihiyar hanya.
Ƙorafin, wadda ƙungiyar kare gaskiya da adalci ta Public Integrity Forum, PIF ta aikewa da hukumar, na ɗauke da sa hannun Daraktan ta, David Ekele Okonjo.
Jaridar Daily Najerian ta rawaito cewar, Ƙungiyar ta kuma nemi ICPC, da EFCC da hukumar Kula da Ayyukan ’Yan Sanda PSC, kan su haɗa kai wajen gudanar da bincike kan kadarorin da ake alakanta tsohon jami’in da mallaka a Kano, Abuja da Lagos, tare da duba mu’amalarsa da bankuna da hanyoyin samun kudinsa.
Kungiyar ta kuma ce bayanan da ke hannu su sun nuna yiwuwar aikata laifuka da suka haɗa da almundahana, cin hanci da dai sauran su.
Haka kuma, kungiyar ta bukaci a duba tarihin aikin tsohon mataimakin sefeton yan sandan domin gano ko akwai cin zarafi ko karya ka’idojin aikin ’yan sanda a lokacin da yake aikinsa.
Ƙungiyar ta gargadi cewa, irin waɗannan zarge-zarge kan manyan jami’an tsaro na iya raunana amincewar jama’a ga hukumomin tsaron ƙasar nan.
Sai dai zuwa yanzu hukumar ta ICPC ba ta bayar da wata sanarwa ba kan ko ta fara bincike kan ƙorafin ko kuma a’a.
You must be logged in to post a comment Login