Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Mun bankado yunkurin kona gidan gwamnatin Kano- ‘Yan Sanda

Published

on

Rundunar ‘yan sanda jihar Kano, ta ce ta bankado wani shiri da wasu marasa kishin kasa ke yunkurin yi na kona gidan gwamnatin jihar Kano a kan shari’ar da ake ci gaba da yi a kotun koli kan zaben gwamna tsakanin jam’iyyar NNPP da APC.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano, Muhammad Usaini Gumel ne ya bayyana hakan, a ranar Laraba a wani taro da shugabannin kafafen yada labarai, gabanin zaman kotun koli na daukaka kara kan shari’ar kujerar gwamnan Kano da aka shirya gudanarwa yau Alhamis 21 ga watan Disamba, a Abuja.

Gumel ya bukaci kwararrun kafafen yada labarai da su sanar da jama’a yadda ya kamata a kan abubuwan da ke faruwa bisa tsari da gaskiyar labari.

A cewarsa bai kamata a samu tashin hankali a Kano ba, domin maganar tana kotun koli da ke Abuja ba a jihar ba.

Haka zalika Kwamishina ya ce ‘rundunar a shirye take ta murkushe duk wani mutum ko gungun mutane da za su yi yunkurin tayar da zaune tsaye a jihar ta Kano’.

Ya kuma ja hankalin jama’a da su sanar da hukumar a bisa duk wani labarin da suka samu wanda ba su yadda da shi ba cikin hanzari.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!