Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Tsaro: Ganduje ya bada umarnin rufe makarantun kwana cikin gaggawa

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta bada umarnin rufe makarantun kwana goma da ke jihar.

Kwamishinan ilimi na jihar Malam Sanusi Sa’idu Ƙiru ne ya bayyana hakan a wani saƙon murya da ya fitar.

A cewar sa, an ɗauki wannan mataki ne bayan da aka yi nazari, saboda dalilan tsaro na yadda ake shiga makarantu ana sace ɗalibai.

Makarantun da aka rufe sun haɗa da makarantar Sakandiren kwana da ke Ajingi, sai ta mata da ke Sumaila, da kuma wadda ta ke Jogana.

Sauran su ne, makarantar ƴan mata da ke Gezawa, da Sakandiren maza da ke Kafin Mai Yaƙi, da ta Maitama Sule a garin Gaya, da kuma makarantar kwana da ke Kachako.

Sannan akwai makarantar mata da ke garin Ƙunci, da makarantar maza da ke Ƙaraye, da kuma makarantar mata ta Arabiyya da ke garin Albasu.

Kwamishinan ya ce, rufe makarantun zai fara aiki nan take, har sai Gwamnati ta sake bada sanarwa.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!