ilimi
Mun saki sakamakon Dalibai 11,161 cikin 96,838 suka yi gyara a bana- JAMB

Hukumar shirya jarrabawar shiga manyan makarantun gaba da sakandare ta Najeriya JAMB, ta ce ta saki sakamakon jarrabawar dalibai 11,161 daga cikin dalibai 96,838 da suka yi gyara a bana.
Hukumar, ta bayyana hakan ne ta cikin wata sanarwa da mai magana da yawunta Dakta Fabian Benjamin ya fitar ga manema labarai.
Sanarwar ta kuma ce, daliban sun zauna jarrabawar ne a ranar Asabar 28 ga watan Yunin da ya gabata.
A domin haka hukumar ke cewa duk dalibin da baiga sakamakonsa ba ya tura sakon ‘UTMERESULT’ ta kan wannan lamba 55019/66019 daga lambar wayar da ya yi Rijista da ita.
You must be logged in to post a comment Login