Addini
Mun samar da tsari da tsaro ga maniyyata- Hukumar jin dadin Alhazai

Hukumar jin dadin alhazan Kano tace ta samar da tsari da kuma tsaro ga maniyyatan jihar yayin da ya rage kwana biyu a fara gudanar da ibadar aikin hajjin bana.
Shugaban harkokin tsaron aikin Hajjin bana Dakta Mujahiddin Aminudden, ne ya bayyana hakan ta cikin wani sakon murya da ya aiko wa freedom radio daga kasar Saudiyya.
Dakta Mujahidden ya kuma kara da cewa hukumar ta samar da kati na musamman da zai hana maniyyatan shiga shemomin da ba nasu ba, musamman ma wadanda suke shiga shemar da ba tasu ba a filin Minna.
You must be logged in to post a comment Login