Labarai
Mun samu karin kudin shiga-Gwamnatin Kano
Gwamnatin jihar Kano, ta ce, ta samu karin kudin shiga na wata-wata da ake tattara wa a watanni uku da suka wuce.
Mai bai wa gwamnan Kano shawara kan harkokin kudin shiga Farfesa Ibrahim Magaji Barde, ne ya bayyana hakan a zantawarsa da Freedom Radio yau Litinin.
Farfesa Ibrahim Magaji Barde, ya kuma ce, shirye-shirye sun yi nisa wajen kara fadada hanyoyin samun kudin shiga a fadin jihar Kano domin aiwatar da ayyukan ci gaban al’umma.
Rahoton: Nura Bello
You must be logged in to post a comment Login