Labarai
Mun san ana zaftarewa ƴan fansho kuɗin su – Sani Gabasawa
Hukumar Fansho ta jihar Kano ta ce, tana sane da yadda ake zaftarewa kowanne dan fansho kudinsa a ƙarshen kowanne wata.
Shugaban hukumar Alhaji Sani Dawaki Gabasawa ne ya bayyana hakan jim kadan bayan kammala shirin Barka da Hantsi na nan Freedom Radiyo da ya mayar da hankali kan makomar ƴan fansho da kuma bashin da suke bin gwamnatin jihar Kano tsawon shekaru.
Alhaji Sani Dawaki Gabasawa ya ce, ƙaruwar ƴan fansho a jihar Kano ne ya sanya ake yankar wani adadi a cikin kuɗin yan fansho don a sallami wasu.
“A kowanne wata ana samun ƙaruwar waɗanda suke yin ritaya kuma suna buƙatar kuɗin fansho wannan ne dalilin da ya ake yankewa daga cikin kuɗaɗen tsoffin ƴan fansho domin a bai wa sabbin”.
Sani Dawaki Gabasawa ya ƙara da cewa “Duk wanda aka cirarwa kuɗin fansho muna sane da shi kuma za a mayar masa da kuɗaɗen su kuma nan ba da daɗewa ba gwamnatin jihar Kano za ta mayar musu da kudaden su”.
Tsawon shekara guda kenan yan fasnho a jihar Kano ke kokawa kan yadda ake yankar musu kuɗin su a kowanne wata ba tare da wani dalili ba.
You must be logged in to post a comment Login