Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

‘Yan jaridu sun nemi Ganduje ya biya bashin ‘yan fansho

Published

on

Kungiyar ‘yan jaridu ta kasa ta bukaci gwamnatin jihar Kano da ta biya tarin bashin kudaden ariya-ariya da garatuti da ‘yan fansho a jihar ke binsu na tsawon watanni.

Hakan na cikin wata sanarwar ce ta hadin guiwa da shugaban kungiyar ta NUJ reshen jihar Kano, Abbas Ibrarim da sakataren kungiyar, Abba Murtala suka fitar, jim kadan bayan kammala taron kungiyar a yau Asabar.

Tun a watan Yunin da ya gabata ne shugaban kwamitin amintattu da ke kula da asusun ‘yan fansho na jihar Kano, Alhaji Sani Gabasawa ya bayyana cewa, gwamnatin ta gaza biyan kudaden ‘yan fansho wanda ya kai sama da naira biliyan ashirin.

Sanarawar ta bukaci gwamnatin da ta yi duba kan halin da ‘yan fansho ke ciki na rashin biyan su kudaden su.

Karin labarai:

Gwamnatin jihar Jigawa ta fara biyan ‘yan Fansho

Kudin da ‘yan fansho ke amsa ya yi kankata- Hamza Sule Wuro-Koki

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!