Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Mun sauyawa mataimakan Sufeton ‘yan sanda 24 wuraren aiki – AIG Alkali Baba

Published

on

Babban sufeton ‘yan sandan kasar nan Usman Alkali Baba ya ba da umarnin sauyawa mataimakan sufeto janar-janar guda 24 zuwa shiyyoyi daban-daban na kasar nan.

Wannan na cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar mai dauke da sa hannun mai magana da yawunta na kasa Frank Mba.

Sanarwar ta ce tsohon Kwamishinan ‘yan sandan birnin tarayya Abuja Bala Ciroma da aka daga likkafarsa zuwa mataimakin sufeto janar, yanzu an mayar da shi shiyya ta 7 da ke Abuja.

Sauran wadanda sauyin ya shafa sun hada mataimakin sufeto janar na ‘yan sanda Dasuki Galadanci da aka mayar zuwa shiyya ta 17 da ke Akure a Jihar Ondo.

Sauyin na su dai ya fara aiki nan take kamar yadda sanarwar ta tabbatar.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!