Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Kaduna

Mun shiga bincike don gano waɗanda suka kashe Abdulkarim Na’Allah – Ƴansanda

Published

on

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna ta ce, ta shiga bincike kan kisan gillar da aka yiwa Abdulkarim Ibn Na-Allah mai shekaru 36, ɗa ga Sanata Bala Na’Allah.

A wata sanarwa da mai magana da yawun ƴan sandan jihar ASP. Muhammad Jalige ya ce, ƴan bindiga sun shiga gidan marigayin da ke unguwar Malali, inda suka hallakashi.

Kazalika ƴan bindigar sun tafi da motarsa ƙirar Lexus SUV, wadda har yanzu ba a kai ga ganota ba. ASP. Jalige ya ce, marigayin ƙwararren matuƙin jirgin sama ne, saɓanin labarin da ake yaɗa wa, na cewa marigayin Kyaftin ɗin soja ne.

A ƙarshe rundunar ƴansandan ta miƙa saƙon ta’aziyyarta ga iyalai da ƴan uwan marigayin.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!