Labaran Kano
Mun yi tsayuwar daka wajen bibiyar rahoton kudi- Dan majalisar Kano
Majalisar dokoki ta jihar Kano ta kammala sauraron rahoton kwamitin da ta kafa na bibiyar mu’amalar kudi da aka gudanar a ma’aikatun gwamnatin jihar Kano PAC na shekarar 2012.
Majalisar dai ta dauki tsawon kwanaki tana sauraron karanto rahoton mamba mai wakiltar karamar hukumar Doguwa Salisu Ibrahim Muhamma shugaban kwamitin ke karantawa inda a zaman majalisar na yau Laraba ya samu nasarar kammala ranta rahoton.
A tattaunawarsa da manema labarai bayan kammala gabatar da rahoton kwamitin na , shugaban kwamitin, Salisu Ibrahim Muhammad ya ce, kwamitin ya yi tsayuwar daka inda daga fara aikinsa ya samu nasarar yin aiki mai tarin yawa sabanin yadda ake tafiyar da aikin a baya.
Haka kuma ya kara da cewa, a yanzu haka ma’aikatun gwamnatin na aiko da rahotonnin kudaden da suka kashe a shekara sabanin shekarun baya da wasu ke shafe shekaru 2 zuwa 3 ba tare da sun aikewa majalisar ba.
Majlisar zartaswa ta amince da fitar da fiye da naira biliyan dari don gudanar da gyaran wasu tituna
Da dumi-dumi-Majalisar dokoki ta Kano ta tsige shugaban masu rinjaye
Gobara ta tashi a gidan dan majalisar wakalai na jihar Zamfara
Wakilinmu na majalisar dokokin jihar Kano Auwal Hassan Fagge, ya ruwaito cewa kwamitin ya ce zai fara bibiyar hada-hadar kudin ta shekarar 2013 a mako mai kamawa kasancewar akwai sauran wadanda ba a bibiya batun a baya.
You must be logged in to post a comment Login